Lafiya Ta Samu: Jaruma Maryam Yahaya ta shilla ƙasar Dubai (hotuna)
A cikin watan Yulin shekarar 2021 ne aka dinga yaɗa hotuna tare da labarin rashin lafiyar tauraruwar Kanywood, inda wasu ke cewa an yi mata asiri ne akan ɗaukakar da ta samu a masana’antar.
Labarin rashin lafiyar Maryam ɗin ya ɗauki hankalin al’umma musamman a shafukan sadarwa na zamani. Sai dai jarumar ta bayyana cewa tana fama da cutar maleriya da taifod.
Jaruma Maryam Yahaya
Inda ta ce ba gaskiya bane kan raɗe-raɗin da ke cewa an yi mata asiri ko jifa.
tun a lokacin hotunan sunka jawo cece kuce wanda ya sanya irin tun jikinta bai murmure sosai ba mutane da har abokan sana’antar suke bata shawara ta dauka daukar hotuna sai ta samu lafiya.
Inda wasu kuma suke bata shawara da cewa wannan ya zamo izna a gareta ta tuba ta komawa ubangiji ta daina wannan sana’ar amma dai yanzu kam tana dubai wajen dauke farali.