Kannywood

Ko ‘Yan Kannywood Za Su Kai Karar Mawaki Naziru Kotu Kan ‘Bata Musu Suna? – Imam Aliyu Indabawa

sarkin waka Nazir M Ahmad
Sarkin waka Nazir M Ahmad

Maganar Mawaki Naziru M Ahmad cewa akwai da yawan ‘yan mata wadanda sai an yi zina da su ake saka su a fim gaskiya ce. Na ga har rantsuwa ya yi kan maganar tasa bari mu jira cikin ‘yan fim ko za a sami masu mazantakar da zai fito ya rantse cewa bai taba lalata da mace kafin ya saka ta cikin fim dinsa ba. Za ku gani wallahi ba za su rantse ba domin aikinsu ne lalata yaran mutane, idan karya Naziru ya yi muku to ku kai shi Kotu kawai.

Ban cika magana kan lamura marasa muhimmanci ba, ban so kuma na yi magana kan 2k-4k da wata tsohuwa ta ce ana biyanta kudin aikin fim ba. Amma maganar Naziru ta taba min inda ke min ‘kai’kayi.

Na rantse da Allah ‘yan matan fim din nan karuwai ne masu lasisi wadanda ‘yan siyasa da masu hannu da shuni ke lalata da su suna ba su makudan kudade, shi ya sa kuke ganin su suna fita kasashen waje suna wada’ka da kudi son ransu, ga ma*d’igo da ya mamaye harkar wanda shekarar da ta wuce sai da wata ta tona asirin wata fitacciyar jaruma, ga shaye-shaye da aka shaidi yaran nan mazansu da matansu ke aikatawa.

Su ma mazan da yawansu ba mutanen kirki ba ne, ba su da aiki ban da zinace-zinace da lalata tarbiya. Kuna saka yara mata a fina-finanku kuna zina da su kuna kuma kai su wa ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suna ba ku kudi. Alhalin kun ki saka ‘ya’yanku kannenku ko matanku cikin harkar kun killace su a gida. Kuna kawalcin ‘yan mata ana ma*digo da su. Mu dai ‘yan hausa fim ba abin da suka amfana mana ban da lalata tarbiya da d’abbaka shaidanci da wanzar da yahudanci. Allah ya sani ina matukar kyamar abubuwan da wadannan mutane ke aikata mana cikin al’ummarmu.

KARANTA WANNAN
Ladin cima: Ka Fara Yiwa Yayanka wa’azi kafin ka fito kana Surutai Nuhu Abdullahi Ga sarkin waka

Babban goro sai magogin karfe :Sarkar gwal ta Naira miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikarta
Ban son na kama suna, amma akwai munanan labarai da wani dan fim din ke sanar da ni, wanda na kara tabbatarwa cewa yaran nan shaidanu ne ko saboda fasikancinsu dole mu yi ta gamuwa da musibu. A haka ne wani d’an iskan Yaro mai suna Aminu Shariff Momo ke cewa wai da a gina masallaci da islamiyya gwara a yi film. Ke nan yana nufin da a dinga sallah ana koyawa yara tarbiyya da karatun Alqur’ani gwara a dinga assasa karuwanci, ma*digo, zinace-zinace da shaye-shaye a Kano.

Ko watanni biyu da suka wuce an sami wani Sanata a Kano mai suna Barau I. Jibrin inda ya tara wadannan ashararun yara ya kashe musu kusan miliyan dubu daya, wanda a sannan ne mutane ke mutuwa saboda rashin kudi a Asibiti wasu na mutuwa saboda yunwa, a lokacin ne na yi rubutu har aka sami wani mutum mai suna Hamisu Iyantama ya fito yana min barazanar lallai na janye kalamaina, abin da ban yi ba ke nan. Sai dai tarihi ba zai manta da barnar da su Iyantama suka yi wa al’umma ba. A shekarun baya ne Yahu*dawan Amurka suka ba wa Hamisu Iyantama kwangilar shirya fim na ‘batanci ga ad*dini da tarbiyya wanda gwamnatin Malam Shekarau karkashin hukumar tace fina-finai wacce Abubakar Rabo Abdulkarim ke jagoranta ta kwamushe Iyantama zuwa Kurkuku amma Amurka ta shiga ta fita aka sake shi. Mutum mai mummunan tarihi irin wannan ne zai dinga barazana saboda wani Sanata mai suna Barau Jibril wanda ya butulcewa maigirma Gwanma Ganduje Khadimul Islami.
Da yawan yaran nan ‘yan fim ashararu sun ya’ki Gwamna Ganduje lokacin zabe, saboda gwamnatinsa na daukan matakin magance ‘bata tarbiyyar da suke yi karkashin hukumar Hisba da hukumar tace fina-finai.

Allah Ya Shiryi Wadannan Yara Idan Ba Za Su Shiryu Ba Ya Yi Musu Abin Da Suka Cancanta Da Shi.
Indabawa Aliyu ImamMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button