Kaji Rabo : Yadda ƙawar amarya tayi wuff da angon ƙawar ta a ranar biki
Lamarin ya faru ne a unguwar Katsinawa ta Mararraba a jihar Nasarawa. Shaidun ganin da ido sun tabbatarwa da shafin Northern Hibiscus cewa lamarin ya auku ne yayin da amaryar ta ce ta fasa auren inda ƙawarta ba tayi wata-wata ba ta ce ayi da ita.
Nan take aka ɗaura musu aure inda wani mutum ya ba ango kyautar naira miliyan biyu nan take. Mai unguwar wurin ya yiwa ango kyautar kayan ɗaki yayin da abokanan ango su ka biya sadakin naira dubu ɗari da hamsin nan take.
View this post on Instagram
A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin an nuno amaryar da ta ce ta fasa auren kwance a gadon asibiti cikin halin damuwa. A yayin da a wata dauƙa daban kuma aka nuno ƙawar ta wacce aka ɗauran auren da ita a wajen biki cikin annashuwa.
Ga kadan daga cikin martanin da mutane sunka bayyana.
@asmaulhusnarh:Masu daukan video dinnan akwai yan gulma yasin
@Kafigwamna : Insha Allah tana tashi zataji har amaryan tayi ciki
@marbella_cares_nd_more: Wannan qawar ba qawar arziki bace wlh haba.
@maouol_ml:Wai jinyar ta mecece?
@deelah_sambo:Kash! Abu baiyi kyau ba… What we forget it is that she’s not his wife, it’s not written in their destinies. Allah ya ba ango da amarya zaman lafia, ita kuma mai jinya Allah ya bata lafia ya kawo mata mafita
Wannan shine ake cewa baraboba Allah yaba ango da amarya zaman lpy ita kuma Allah yabata lpy Allah baiyi matar sa bane shiyasa