Gobe Juma’a Buhari zai sanya hannu a kundin gyaran dokar zaɓe
Daily Nigerian Hausa ta tuno yadda jam’iyyar adawa ta PDP da sauran kungiyoyin farar hula su ka matsa wa Buhari lamba bayan da ya yi shakulatin ɓangwaro da kundin dokar.
Amma kuma wasu sahihan majiyoyi da ga fadar Shugaban Ƙasa sun tabbatar wa Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN, cewa a gobe Juma’a Buhari zai rattaba hannu a kundin dokar da misalin ƙarfe 12 na rana.
A ranar 31 ga watan Janairu ne dai Majalisar Taraiya ta muƙawa shugaban ƙasa kundin dokar a karo na biyu bayan yi masa kwaskwarima, amma sai shugaban ya ɗauki tsawon lokaci bai rattaba hannu ba.
Majiyoyin fadar Shugaban Ƙasar sun baiyana cewa an kammala duk wani shirye-shirye domin sa hannu a dokar inda hakan zai kawo karshen duk wani cece-kuce.
A tuna cewa a ranar 21 ga watan Nuwamba 2021 shugaban ƙasa ya ƙi sanya hannu a kan kundin dokar wanda ya bada dalilin cewa, yin zaɓen ƙato-bayan-ƙato zai lashe maƙudan kuɗaɗe sannan kuma da rashin tsaro da ke addabar ƙasa.
Ya kuma bada dalilin cewa ƴan siyasa za su yi amfani da hakan su riƙa yin rashin adalci a zaɓe.