LabaraiUncategorized

FUTO ta maka ASUU a kotu kan ƙin amincewa da Pantami a matsayin Farfesa

FUTO ta maka ASUU a kotu kan ƙin amincewa da Pantami a matsayin FarfesaShugaban Jami’ar Fasaha ta Taraiya a Owerri, FUTO, Farfesa Nnenna Oti ya bayyana cewa hukumar makarantar ta maka Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU a kotu domin ƙin amincewa da ƙarin matsayin Farfesa da ta yi wa Dakta Isa Ali Pantami.
Tun da fari dai, ASUU ɗin ta yi barazanar ɗaukar mataki a kan FUTO sabo da ta baiwa Pantami matsayin Farfesa duk da cewa ya na aiki a Gwamnatin Taraiya a matsayin Minista.
Da ya ke shaidawa jaridar The Nation a jiya Litinin, Shugaban jami’ar ya ce tuni su ka shigar da ƙara a kan lamarin.
Bayan haka, wani babban ma’aikaci a jami’ar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa jaridar cewa ASUU ba ta da ikon sa baki a batun da ba ta da hurumi a kai.
“Kamar yadda ita ASUU ba ta da ikon da za ta fadawa majalisar jami’ar kan wa za ta ciyar gaba, ba ta da ikon da za ta gayawa jami’ar sharuddan da za ta bi ta bada matsayin Farfesa ba.
“A fannin Shari’a, ba za ka janye abinda ba ka da shi ba. ASUU ba ta ikon kula da harkokin naɗin muƙami da ci gaban matsayi.
“Hukumar kula da Ilimin Jami’a 5a Ƙasa, NUC ce ke da alhakin irin waɗannan abubuwan, kuma ko wacce jami’a ita ta ke shimfida sharuddan ta,” in ji majiyar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button