Baya Hallatta Ga Macce Marar Aure ta sanya Hofa ta Fita fira/zance
Da farko A Mazhabar Shafi’iyya da Malikiyya, da Hanabila gaba dayansu sun tafi kan cewa fuskar mace al’aura ce kuma dole ne ta rufe fuskarta wajibi ne, bude fuska haramun ne.
Albany ya kawo wannan maganar a littafinsa Jilbab cewa, “Wajibine Macce ta Rufe fuskarta.” Haka ma mai littafen Tarbiyatul Aulad Nasihil Ulwan shima yakawo wannan maganar.
Mazhabar Hanafiyya ce kawai suka ce fuskar mace ba dole ba ne ta rufe fuskarta ya halasta ta bude fuskarta In dai ba’a tunanin fadawa cikin fitina. In an tabbatar ana lokacin aminci to ba komai tana iya bude fuskar ta.
Imam Ibn Katheer Ya fada Cewa, BAYA HALATTA GA MACCE TA BAYYANAR DA FUSKARTA SAI A GUN MUHARRAMIN TA (Tafsir Ibn Katheer 3/274)
Haka An tambayi manyan Malamai masu bayarda Fatawa a Saudiya cewa, “Ko Macce zata Iya yin Kwalliya?.”
Suka bada amsar cewa, “Hakika Babu abinda zai hana macce Yin kwalliya sai dai kuma baya halatta ga macce tayi kwalliya ga wasu mazan wayanda ba muharramant ba.” (Fataawa Al-lajnah al-Daa’imah (17/129).
Dukan Malumman Sunna Sun tafi akan Cewa, Baya halatta ga macce marar aure ta yi kwalliya (musamman da abinda zai cenja mata fatar jiki), domin idan ba’kace,Idan Wani namiji ya ganta yana sonta aure Zaiyi tunanin fara ce, ta dalilin wannan hodar da ta sanya, wanda kuwa a aure ba’a bukatar boye kama.
Haka kuma matar aure zata iya yin kwalliya amma idan daga ita sai ‘yan uwanta mata ne a gidan ko kuma muharraminta, (Miji, Kanenta,Yayanta, Mahaifinta, Mahaifin mijinta dasauransu).
Haka kuma a cikin Fataawa Al-lajnah al-Daa’imah, Sun bayyana Cewa, Matar Aure zata iya yin kwalliya makawar Babu wanda zai ganta, amma idan wanda ba muharraminta ba ya ganta to ana kwautata zaton za’a iya rubuta mata Zunubin fita “Tabarruj”.
Bama yin kwalliya ta fita ba bude fuskarta ma ta fita wasu malumma suna ganin kuskurene.
Shiekh Usaimin ya ce, “fuskar mace nan ne matattarar fitina kuma nan ne wurin farko da mace zata rufe kuma mutane da dama suna sakaci wajen barin yaran su na fita fuskar su a bude wanda bai kamata ba. (Usratul muslima).
Shima sheikh Muhammad bn AbdulMaqsud yana da fahimtar mace ta rufe dukkan jikinta baki daya kar ta bar komai sai dai idonta da za ta ga hanya, hujar sa hadisin bn Mas`ud wanda Imamu Tirmidhi yaruwaito da isnadi igantacce. “Mace al`aurace mu kuma an umurce mu da mu rufe al`aura” (Fatawaa Mar`atul Muslimah 602)
A karshe Ina cewa, Mai son ganin bayani sosai sai ya duba littafin Imamul Kurdubi ko Tafsirin Baydawi ko ibn Kasir ko Mahasinu Tanzil ko ka duba Jilbabul mar atil muslimah na Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany ko Audatul hijab da Libasul Yaum na Ammru da Sarimul mashur alt Tabarurj.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 03-02-2022
One Comment