LabaraiUncategorized

Au’zubillahi: An kashe wata mata da raunata ƴaƴanta biyu a Kano

Au'zubillahi: An kashe wata mata da raunata ƴaƴanta biyu a KanoAllah yayi masa sauki wannan al’amari abubuwa sai faruwa kawai suke a birnin kano da ke arewacin nijeriya inda jaridar bbchausa na kawo wani rahoto marar dadi ga abinda suke cewa.
“Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe wata mata a gidanta da ke Unguwar Kadawa a Kano.
Waɗanda suka kashe matar matar mai suna Rukayya sun ji wa ƴaƴanta biyu rauni.
Abin ɗaure kai game da yadda aka kashe ta shi ne babu wanda ya san takamaimai lokacin da lamarin ya faru, sai dai ana kyautata zaton sun shiga gidan ne bayan magariba a ranar Asabar.
An dai ɗage zaman ne sakamakon rashin Lauyan da zai kare wadanda ake zargi da kisan hanifa Abubakar
An shiga jimami: Jama’a sun shiga tashin hankali da zub da hawayen yayinda amarya ta rasu ana daf da daurin aurenta
Duk da cewar mazauna unguwar sun ki yarda BBC ta naɗi muryoyinsu, amma sun bayyana cewa akwai magina a jikin gidan da shagunan sayar da kayayyaki haka kuma a iya saninsu ba su ga shigar wani baƙo gidan ba haka kuma ba su ga fitar waɗanda suka gudanar da wannan aika-aika ba.
Sai bayan da mai gidanta ya dawo ne sannan aka san halin da ake ciki. Ana zargin da taɓarya suka daketa a kai har wuri biyu, sannan suka daki ɗanta a kansa sau ɗaya. Sai ƙurjewa da aka samu a fuskar wadda take shayarwa.
Mijin marigayiyar ya gaza yin magana saboda halin da yake ciki.
Yanzu haka babu kowa a gidan marigayiyar kuma ana zaman makoki a gidan iyayen marigayiyar da ke Unguwar Madatai a cikin birnin Kano.
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce tana gudanar da bincike.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button