Labarai

An sauke ni daga mukamin Ministar Ingila saboda kasancewa ta Musulma, kuma nace Allah daya ne – Nusrat Ghani

An sauke ni daga mukamin Ministar Ingila saboda kasancewa ta Musulma, kuma nace Allah daya ne – Nusrat GhaniTsohuwar ministar sufuri ta Birtaniya, Nusrat Ghani, tace, takura mata akayi tilas ta sauka daga mukaminta, lokacin da akayi garan bawul a gwamnatin Birtaniya, a shekarar 2020, kawai dan ita Musulma ce.
A cewar yar jamiyyar ra’ayin rikau din (conservative ), kuma yar zauren majalisa; lokacin da tana hira da jaridar Sunday Times, a ranar Litinin.
Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin jami’an gwamnatin Birtaniya a shekarar 2018
A shekarar 2018 Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin kunshin jami’an gwamnatin Birtaniya. Ta zama ministar sufuri a gwamnatin, a karkashin babban minista, Theresa May.
Kamar yadda Jaridar Labarunhausa na ruwaito cewa amma a watan Fabrairun shekarar 2020, sai aka fitar da Nusrat Ghani din daga jerin kunshin gwamnatin, yayin da sabon babban minista Boris Johnson ya kafa sabuwar gwamnati.
Nusrat Ghani ta shaidawa Sunday Times cewa, da ta tambayi bulaliyar majalisar dalilin da yasa aka cireta daga cikin jami’an gwamnatin, sai yace; “an bijirar da maganar musulunci a matsayin matsala, yayin da ake tattaunawa akan garan bawul din gwamnatin. Saboda haka kasantuwarta musulma, hakan ya sa da yawa basuji dadi ba”.

Kasantuwarki Musulma yana da mummunan tasiri a garan bawul din. Wasu mambobin ma an wulakantasu domin sun Musulunta.”

Tace:
Wannan kamar naushi ne a ciki. Naji haushi kuma naji kamar an zare min laka.

Dan majalisar da aka zaba daga yankin Wilden na Birtaniya , yace “za’a koreshi daga jamiyya, kuma mutuncinsa zai zabe ” Idan ya kambama maganar.

Mark Spencer ya musanta wannan magana
Bulaliyar majalisar, kuma dan jamiyyar ra’ayin rikau din, Mark Spencer, ya musanta zargin da aka fitar a ranar Juma’a, wanda yake zayyano kagen da bashi da tushe balle makama, akan Nusrat Ghani din, wanda ba tun yanzu ake fadar su ba.

Wannan kagen gaba daya karyane, kuma ni ina ma kallonshi a matsayin bata suna” ya fada a twitter.

Spencer yace, shi bai taba gayawa Nusrat cewa an cireshi daga ma’aikata, saboda shi Musulmi bane.
A wani bangaren, ministan ilimi na Burtaniya, Nadeem Jahai, yace wannan zargin ya kamata ayi bincike akai.
A shafinsa na twitter yace, babu wani gurbi daya bada dama a jamiyyar su ta (conservative) mai ra’ayin rikau, da a nuna kiyayyar Musulunci ko wata kabila. Wannan zargi dole ne ayi bincike.
Shugaban jamiyyar adawa ta Labour party, Carestarmer yace, dole ne a bincika wannan zargi na Nusrat Ghani.

Abin kaduwa ne a karanta irin wannan abu” data rubuta a twitter.

Tun farko a ranar, mai gabatawa na jamiyyar ra’ayin rikau, William Rudd, ya zargi babban minista da “daura masa jakar tsaba” inda yan majalisar ke san cire shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA