Labarai
An ɗage shari’ar kisan Hanifa
Babbar kotun jiha mai Lamba 5 ƙarƙashin mai sharia Usman Na-abba ta ɗage ci gaba da shari’ar kisan Hanifah.
An dai ɗage zaman ne sakamakon rashin Lauyan da zai kare su.
A zaman kotun na ranar Litinin an ɗage shari’ar zuwa 14 ga watan Fabrairu.
Kamar yadda freedomradio na ruwaito.,Kotun ta sake gabatar da Abdulmalik Tanko da sauran mutum 2 da ake zargi da laifin kisan ɗalibar ƙarƙashin kwamishinan shari’a Barista Musa Abdullahi Lawal.
Waɗanda ake zargin sun haɗar Abdulmalik Tanko da Hashim Ishak da Fatima Musa jibril.