Almundahanar N73.7m: Kotu ta yanke wa tsohon babban akanta na Hukumar Alhazai shekara 7 a gidan yari
Daily Nigerian ta ruwaito mai Sharia Mu’azu Abubakar na Babbar Kotun Jihar Bauchi ne ya yanke musu hukuncin bayan da Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta yankin Jihar Gombe ta ka kama su da laifuka biyar da su ka haɗa da haɗin baki da kuma yin sojan-gona.
Ma’aikatar Kuɗi da Ci gaban Tattalin Arziki ta jihar ce ta kama su biyun da laifin da fitar da shaidar biyan kuɗi da rasiti na bogi a matsayin shaidar biyan kuɗin Hajji na 2019 ga maniyyata.
Haka kuma an kama su da laifin ƙin saka N73, 715,286.62 a asusun Hukumar Hajji ta Jihar Bauchi.