Labarai

Ajali: Matarsa Ta Kashe Shi Ta Hanyar Caccaka Masa Wuka

A daren yau Asabar ne wani magidanci mai suna Ibrahim Ahmed (Mai Unguwa) ya gamu da ajalinsa sakamakon caccaka masa wuka da matarsa mai suna Atika ta yi.Ajali: Matarsa Ta Kashe Shi Ta Hanyar Caccaka Masa Wuka
Lamarin, wanda ya auku a yankin Unguwar Yerima dake garin Mararrabar Abuja da jihar Nasarawa, binciken RARIYA ya gano cewa matar ta yanke wannan danyen hukuncin ne saboda kara aure da mijin nata ya yi.
Ana sa ran za a yi jana’izar mamacin a safiyar gobe Lahadi, inda ita kuma matar take tsare a hannun hukuma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button