Labarai
Ƴansanda A Katsina Sun Kama Matar Da Ke Yi Ma Ƴan fashin Daji Girga
Advertisment
Rundunar ƴan sandan jahar Katsina ta ce ta yi nasarar kama wata mata da suke da zargi da yi ma yan ta’adda girka.
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Gambo Isah ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis ɗin nan a farfajiyar hedikwatarsu da ke Katsina.
Ya ce sun kama matar mai suna Fatima Alhaji Bammi tana yi ma ƴan ta’adda girka don kar bindiga ta kama su.
SP ya ce daga cikin mutanen da ta yi ma girkar harda wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da ake kira Sani Mohindinge.
Amma a lokacin da ake tambayar matar ta ce ita lokacin da ta yi mashi wannan taimako ana cikin zaman lafiya ba yanzu ba ne ta yi masu girkar
Advertisment