Labarai

Ƴan Sanda sun tabbatar da fashewar bam a Kaduna

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da fashewar bam a jiya Lahadi da daddare a unguwar Kabala ta da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu.Ƴan Sanda sun tabbatar da fashewar bam a Kaduna
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Kakakin rundunar, Mohammed Jalinge ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.
Ya ce ana da tabbacin fashewar bam ce da ta faru da misalin ƙarfe 9:45, inda ya ƙara da cewa fashewar ba ta samu kowa ba sabo da babu kowa a cikin ginin da abun ya fashe.
Ya ƙara da cewa tuni jami’an cire bam su ka isa gurin domin yin nazari.Jalinge ya yi alkawarin cewa zai sanar da sakamakon nazari da binciken da a ka yi da zarar an kammala.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button