Ƴan Sanda sun damƙe likitan Turji da wasu ƴan fashin daji 39
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Sokoto ta cafke wani likita mai suna Abubakar Hashimu, wanda ya yi wa ƙasurgumin jagoran ƴan fashin dajin nan mai suna Bello Turji lokacin da sojoji su ka ji masa raunuka a wani hari da su ka kai masa shekaru 3 da su ka wuce.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Sokoto a jiya Litinin, Ahmed Zaki, Mataimakin Sifeto-Janar ɓangaren aiyuka, Ahmed Zaki ya ce an ka Hashim ne tare da wasu mutane 36.
Wasu daga cikin waɗanda a ka kama sun haɗa da ,Musa Kamarawa, Bammi Kiruwa, Zayyanu Abdullahi, Hardo Yunusa da Samuel Chinedu da sauran su.
A cewar Zaki, an yi kamen ne tsakanin 20 ga watan Janairu da 29 ga Janairu.
Ya ƙara da cewa ƴan sandan ‘Operation Sahara Storm ne su ka cafke ƴan ta’addan bayan da su ka kai sumame a Illela, Rabah, Isa da Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.
Ya ce a yayin sumamen, an kama mutum 37 tare da kayan laifi da dama a wajen su.
A cewar Zaki, dukkan su suna da alaƙa da Turji kuma sun amsa cewa suna da hannu a ta’addancin fashin daji da a ke yi.
A ƙarshe, Zaki ya ce ana ta bincike a kan lamarin, inda ya ƙara da cewa ana kammala binciken za a gurfanar da su a gaban kotu domin su girbe abinda su ka shuka.