Yadda Makwabcina Ya Sace ’Yata, Ya Kasheta Bayan Karbar Miliyan 3’ Kaduna
Aminiya ta ruwaito cewa ,Al’umma na ci gaba da zuwa jaje gidan Alhaji Shu’aibu Wa’alamu Wamban Dawaki, mahaifin yarinya mai shekara takwas da haihuwa da ake zargin wani makabcinsa ya hada baki da masu garkuwa wajen kasheta bayan karbar miliyan takwas a matsayin kudin fansa.
Lamarin dai ya faru ne a birnin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Ana dai zargin makbcin Wa’alamu da kisan yarinyar mai suna Asama’u, bayan ya hada baki da masu garkuwa da mutane, inda suka kasheta bayan sun karbi kudin fansar nata.
Mahaifin na Asama’u ya ce tun a ranar tara ga watan Disamban aka sace ’yar tasa, kuma tun lokacin suka sanar da ’yan sanda tare da kai cigiya wurare daban-daban.
Sai dai ya ce daga baya an fara kiran lambarsa, inda aka bukataci ya biya Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansarta.
Ya ce, “Daga baya mun basu Naira miliyan biyu. Bayan an kai musu kudin har unguwar Rigasa da ke Kaduna, sai suka ce sai an kara ba da da miliyan daya da dubu 45 kafin a sakota.
“Duk bayan mun biya kamar yadda suka bukata, sai kuma aka bugo mun waya a ranar Laraba, 19 ga watan Janairun 2022 da safe cewa sun kasheta, daga nan sai aka kashe waya.”
Alhaji Shu’aibu Wa’alamu, ya ce tun bayan sace yarinyar, suna bin umurnin ne kawai gudun kada a hallakata amma sun riga sun gama sanin wanda ya saceta.
Mahaifin ya ce sun tabbatar da hakan ne sakamakon kwararan hujjojin da suke da su cewa makwabcin nasa ne ya sace diyar tasa.
Yanzu haka dai jami’an ’yan sanda masu yaki da muggan laifuka na IRT suka kama wanda ake zargin domin fadada bincike.