Labarai

Karshen Bello turji yazo a gabanmu Sojoji sunka tarwatsa yaransa (hira da Ganau)

A makon nan ne ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan da aka fi sani da Bello Turji ya saki wasu gomman mutane da suka daɗe suna tsare a hannunsa.
Bello Turji dai na daga cikin manyan ƴan fashin dajin da ke Najeriya da ake nema ruwa a jallo sakamakon irin hare-haren da yake kai wa shi da yaransa.
Wani daga cikin sama da mutum 50 da Bello Turjin ya saka mai suna Ahmad Abdulrazak, wanda yaran Bello Turji suka sace a hanyar Kaura Namoda zuwa Sabon Birni ya ce sun sha baƙar wuya a hannun Turji.
A wata hira da ya yi da tashar Mai Biredi TV ta Youtube, ya bayyana cewa ya shafe kwana 32 a hannun masu garkuwan, amma duk tsawon waɗannan kwanakin bai samu ganin uban gayyar ba wato Bello Turji.
https://youtu.be/yIb-Zga2m_U
Ahmad ya bayyana cewa ƴan bindigan sun faɗa musu abubuwa da dama, inda daga ciki suke yawan ba su labarin cewa a rayuwarsu babu abin da suke tsoro kamar jirgin soji.
Ƴan bindigan sun shaida masa cewa don jami’in tsaro ya je wurinsu a ƙasa lallai za su illata shi, ya kuma bayyana cewa har nema suke sojoji su zo wajen su a ƙasa domin su illata su.
“Da sun ga jirgin sojoji za su ɗauremu da kaca su ƙara tsuke mu su tsere su je wajen dutsi su ɓoye,” in ji Ahmad Abdulrazak.
Ya ƙara da cewa sojoji ba sa shiga cikin dajin a ƙafarsu , jirgi ne ke shiga.
Ya bayyana cewa sun ga jirgin soji ya shiga daji sau da dama har ya taɓa jefa musu bam ɗin da ya kusan illata su sakamakon wutar da ta tashi bayan jefa bam ɗin da jirgi ya yi.
Ahmad ya tabatar da cewa bam ɗin da jirgin yaƙin soji ya jefa a cikin daji har sai da ya ƙona makarantar Turji da kuma kayan abincinsa.
Ya bayyana cewa jirgin bai illata ko mutum ɗaya ba cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, amma kuma ya illata wasu daga cikin yaran Turji da makamansu inda har mutum guda ya rasu.
Ahmad ɗin ya bayyana cewa ya ji ɗaya daga cikin yaran Turjin na cewa mai gidansu ya bayar da kuɗi naira miliyan biyu a kai ɗaya daga cikin yaransa da jirgi ya illata zuwa asibiti.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA