Labarai

Hotuna: Ƴan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Hanifa

Jami’an ‘yan sanda sun damke mai wata makaranta mai zaman kanta mai suna Noble Kids School da laifin sace wata dalibar sa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5 tare da kashe ta.
Majiyoyin iyalan yarinyar sun ce yana daga cikin mutanen farko da suka zo jajanta wa iyayenta bayan sace ta, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
“Ya cika da kuka a lokacin da ya ziyarci iyalan domin ta’aziyyar sace yarinyar,” in ji kawun yarinyar, inji Kawun yarinyar mai suna Suraj Sulaiman.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Alhamis ta ce malamin makarantar, Abdulmalik Tanko ne ya sace ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA