Labarai

Da dumi dumi : Yan bindiga sun harbe Jarumar Fim har Lahira

Da dumi dumi : Yan bindiga sun harbe Jarumar Fim har LahiraWASU ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wata jarumar finafinan Nollywood mai suna Ngozi Chiemeke a jiya.
Rahotanni sun ce abin ya faru ne a titin Deeper Life a garin Boji-Boji Owa da ke Ƙaramar Hukumar Ika North-east ta Jihar Delta.
Mujallar Fim ta gano cewa an kashe jarumar mai tasowa ne a shagon ta na sana’ar hadahadar kuɗi na P.O.S.
Mutanen unguwar sun ce su dai sun ji tashin bindiga a wajajen shagon, to amma kafin su kai ɗauki har maharan sun arce daga wurin.
Ba a san dalilin kisan ba.

Ngozi Chiemeke a lokeshin ɗin ɗaukar wani fim
Ngozi Chiemeke a lokeshin ɗin ɗaukar wani fim

An ɗauki gawar Ngozi Chiemeke an kai ta mutuware an aje kafin a yi mata jana’iza.
Kisan gillar ya haifar da babban ruɗani da baƙin ciki a garin, inda mutane su ka riƙa taruwa gungu-gungu su na tattaunawa a kai.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da labarin kisan ga ‘yan jarida, ya ce, “Wasu maza da ba a san ko su wanene ba su ne su ka kashe matashiyar matar, amma an fara ƙoƙarin kama waɗanda su ka aikata wannan abu.”
Mujallar Fim ta fahimci cewa wannan sabon kisan gillar ya faru ne ba da daɗewa ba bayan kisan da aka yi wa Cif Anthony Mkpado, wani ɗan kasuwa mamallakin shagon sayar da littattafai mai suna Mkpado Bookshop da ke kallon reshen bankin First Bank a garin na Boji-Boji Owa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button