AddiniLabarai

[Bidiyo] Martanin Prof Isah Al Pantami kan kisan Hanifa wanda yasa mutane zubda hawaye

[Bidiyo] Martanin Prof Isah Al Pantami kan kisan Hanifa wanda yasa mutane zubda hawayeMinistan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami ya hori mahaifan Hanifah Abubakar, yarinya ƴar shekara 5 da malamin makarantar su ya yi wa kisan gilla.
Pantami ya yiwa mahaifan marigayiya Hanifah nasihar ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya gidan su a yau Lahadi.
Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, inda daga bisani mahaifin ya jagoranci Ministan shiga cikin gida don yi wa mahaifiyar Hanifa da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi.
Malam Pantami ya yi nasiha ga iyayen Hanifa akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan.
Farfesa Pantami, ya roki Allah Ya sanya marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.
Iyayen marigayiya Hanifa Abubakar sun godewa Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da Pantami ya gabatar.
Ga faifan bidiyon nan kasa ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button