LabaraiUncategorized
BABBAN LABARI: Shugaban ƙasar Nigeria Buhari ya yi kyautar Mota kirar golf da kudi dubu dari bakwai (bidiyo da hotuna)
Advertisment
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bawa Malam Umar Small fire kyautar Mota kirar golf da kudin Mai Naira Dubu Dari bakwai.
Malam Umar Small fire shine wanda ya dauki Shugaban kasa Buhari a motar sa ya kaisa gida yayin da Boko haram suka kai masa hari a kawo kaduna a shekaran 2014
Shugaban kasar bai iya tunawa da mutumin da ya tseratar da rayuwar tasa ba sai da mutumin ya fito Social Media yayi korafi.
Duda haka mutane na kallon lallai Malam Umar Small ya taki babban sa’a da ya samu kyautar Mota har da kudi daga shugaban wanda ba’a cika ganin yayi kyauta ba.