Aure Rahama : Matar Aure zainab Bello ta kamala digirin karantu na Mathematics da First Class
Ga wata matar Aure mai suna Zainab Bello Kofa, ta kammala karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello University Zaria, ta karanta Lissafi (Mathematics) ta fito da sakamako mafi daraja a ABU Zaria inda ta samu maki 4.85 -CGPA
Zainab matar aure ce, kuma tana da yara, sai da tayi aure kafin ta fara karatun jami’ah, kuma gashi ta zama the best a ajin Mathematics
Don haka karnukan farautar Yehudawa su dena rudar da mu cewa wai aure yana hana karatu, wannan karya ne da makirci
Muna fatan Allah Ya sanya albarka a rayuwar Zainab da zuriyarta da namu baki daya Amin
A wani bangaren labarin da wasu majiyoyi sun nuna cewa wannan baiwa Allah babban abun mamaki kuma ita hafiza ce domin ta harda ce Alkur’ani mai girma tun tana yar shekara sha daya 11a duniya wanda idan tabbas gaskiya ne to ba abin mamaki bane zata iya samun makin karatunta na lissafi fiye da haka duba da daraja da mu’ujizar Alkur’ani mai girma.
MashaAllah