Kannywood

Anya son kuɗin Alhaji Badamasi zai bari ya auri Junaidiyya?

Anya son kuɗin Alhaji Badamasi zai bari ya auri Junaidiyya?A wannan Alhamis ne 06 ga watan Fabarairun 2022 ne aka dawo haska shirin nan mai dagon zango na barkwanci wato Gidan Badamasi a tashar Arewa 24.
Shirin wanda a zagon baya aka karkere da batun kai ‘yayan gidan Alhaji Badamasi gidan gyaran hali a sakamakon almundahana da sukayi tareda zanbatarshi, inda shi kuwa Alhaji Badamasi ya bayyana kudurinshi na Auren wata santaleliyar yarinya wato Junaidiyya.
Bayan dawowa wannan zangon ne dai Alhaji Badamasi yayi tattali kafa da kafa zuwa gidansu Junaidiyya domin tattaunawa da iyayenta kan batun aurensu da kuma biyan miliyan kudade da tsohon saurayin Junaidiyya ya bukata wanda yace ya kashe mata ne ayayinda yake neman Aurenta.
Saidai a irin son kudi na Alhaji Badamasi yace wannan kudi sunyi mishi yawa, kuma yana tantama ko kudin ma sun kai haka ko kuma A’a.
Abun jira a gani dai shine ko Alhaji Badamasi zai biya wadannan kudade domin samun damar mallakar Junaidiyya a matsayin matarshi ta Aure. Lokaci ne kawai zai tabbatar.
Daga Sani Adamu Hassan

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA