Labarai

TA FARU TA ƘARE: Gwamnan Ekiti da na Jigawa sun kira Ɗanzago da shugaban APC a Kano

TA FARU TA ƘARE: Gwamnan Ekiti da na Jigawa sun kira Ɗanzago da shugaban APC a KanoGwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da takwaransa na Jigawa, Abubakar Badaru, sun kira Ahmadu Haruna Zago da shugaban jam’iyar APC a Jihar Kano.
Zago, wanda a ka fi sani da Ɗanzago, shine shugaban APC, tsagin Sanata Ibrahim Shekarau a Jihar Kano.
A wani yanayi na ɗan hakin da ka raina, da alama dai za a iya cewa ta faru ta ƙare a shugabancin APC bayan da Fayemi, wanda shine Shugaban Muryar Gwamnonin Nijeriya, da Badaru, su ka kira Ɗanzago da shugaban jam’iyar APC a Kano.
A ƴan watannin nan ne dai jam’iyar me mulki a Kano ke fuskantar rikici wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, inda ya haifar da rabuwar jam’iyar zuwa ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje da na tsohon gwamna, Sanatan Kano ta Tsakiya, Shekarau.
Tun a lokacin zaɓen shugabannin jam’iya na jiha a ka samu rabuwar APC gida biyu, inda ɓangaren Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, shi kuma tsagin Shekarau ya zaɓi Ɗanzago.
Sai dai kuma, a ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotu a Abuja ta rushe shugabacin Abdullahi Abbas ta kuma tabbatar da na Ɗanzago a jihar, duk da cewa tsagin Gandujen sun ce za su ɗaukaka ƙara.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamnonin, a yau Asabar, yayin jawabin su a wajen taron cikar shekarar Cibiyar Bincike kan Dimokraɗiyya ta Aminu Kano da ke ƙarƙashin Jami’ar Bayero shekaru 21, kowannen su ya kira Ɗanzago da shugaban jam’iyar APC a yayin shimfiɗa a jawaban su.
Jaridar ta ƙara da cewa, wannan shine karo na farko da a ka ambata Ɗanzago a matsayin shugaban APC a bainar jama’a, tun bayan da a ka yi zaɓen Shugabannin jam’iyar a Kano.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA