LabaraiUncategorized

[Sautin Murya] Yadda halin yan gudun hijira a Zamfara suke cikin ƙuncin rayuwa

[Sautin Murya] Yadda halin yan gudun hijira a Zamfara suke cikin ƙuncin rayuwa“Yau Jabir Mustapha Sambo na BBC Hausa ya kai ziyara kuma yayi hira da ‘yan gudun hijiran Zamfara. Wallahi, babu mai imanin da zai ji halin da matan nan suke ciki, hankalinsa bai tashi ba, idonshi bai cika da hawaye ba. Matan da ‘yan bindiga suka diba, suka ci zarafinsu tsawon lokaci yanzu ba su da abinci, sai dai su ci tafasa kullum. Akwai matar da ruwan surfe suke sha su rayu da ‘ya ‘yanta. Yara kanana suna fa da yunwa da rashin lafiya. Ba su da gurin kwana mai kyau, balle ruwan sha.
Muna kira ga Buhari da Matawalle da suyi gaggawar kafa wa wadannan mata sannanin ‘yan gudun hijira domin su samu gurin kwana da abinci. Wallahi, Buhari da Gwamna Matawalle ku ji tsoron Allah. Ranar kiyama Allah zai titsiye ku akan hakkin wadannan bayin Allah.
Jama’a mu ji tsoron Allah. Idan mahukunta sun ki sauke nauyinsu, lalle ne mu mu tashi mu yi iya-iyawarmu. Wadannan ‘yan’uwanmu ne, kuma suna da hakki akanmu. Wannan rashin Imani yayi isa haka. Mu ji tsoron Allah.
~ Audu Bulama Bukarti”
“A matsayinka na ɗaya daga cikin mahukunta wannan jaha;
– Shin a wannan hali kana iya barci kuwa?
– Shin kana iya murmushi har da dariya?
– Kana amfani da kuɗin wannan jaha wajen biyan naka buƙatu da iyalinka?
A haka yadda ake tafiya a naka tunani babu wata matsala ko wani sakamako ko alhaki da zai biyo baya?
Kana tsammanin shi ke nan za a cigaba da tafiya a haka kuma kai ka zauna lafiya kai da iyalanka babu wani hukunci, jarabawa, musiba ko biyan bashin alhaki daga Ubangiji?
Anya?!
– Abubakar Sadiq”
Ga sautin murya hira da bbchausa tayi da su nan ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button