Rikicin yan tiktok maman Suddenly da Suddenly sunyi mai zafi
Malam critics ya chachaki Rahama sadau
Akan rikicin yan tiktok wanda ake abubuwan na zubda mutunci da debe albarka wanda a koda yaushe muke kira da mutane su daina irin wannan abubuwa da al’adarmu da addininmu bai aminta da shi ba.
Wanda yasan ita dai Suddenly tayi kaurin suna a wannan al’ammari wanda yanzu abun har ya kai ga iyaye.
Rahotanni daga masana’antar Nishaɗi mai tashe ta TikTokwood na cewa, har yanzu dubunnan ƴan masana’antar na dakon jin martanin jaruma Suddenly bayan da wasu jaruman na TikTokwood suka yi mata dukan kawo wuƙa.
Wani sautin murya kuwa na ci gaba da yawo na wadda aka ce mahaifiyar Suddenly ɗin ce na gundumawa jaruma Aisha Zaki da mahaifiyarta ta Maguzawa.
Wata sabuwa ta sake kunno kai bayan da jaruma Sadiya Haruna ta yi barazanar fasa ƙwan wata jaruma da ta ce ta naɗi bidiyon wani babban mutum tsirara lokacin da suke aikata fasiƙanci a Abuja.
Sai dai jaruma Muneerar Abdussalam ta yi martani tana mai cewa da alama Sadiya Haruna da jaruma Teema Makamashi ta ke.
A nata ɓangaren Jaruma Makamashi ta yi kakkausan martani a shafinta na TikTok inda ta musanta cewa ita ce, sannan yi ruwan zage-zage ga Sadiya Harunan, a ƙarshe ma ta ƙalubalanceta kan ta fitar da bidiyon a ga ko wacece.
Yanzu dai ƴan TikTok muna dakon ganin ko wannan bidiyon zai fito?, yayin da wasu kuma ke kiraye-kiraye ga Malam Ibn Sina kan ya kawo ɗauki.
Mu yini lafiya sai kun sake jin mu.
Wani labarin kuma zakuyi yadda malam critics ya Caccaki Rahama sadau a karo na biyu wanda duk zaku cikakken bayyani daga wannan faifan bidiyo da ke kasa.
Sai ku natsu ku saurara.