Kannywood

Mutuwar aurena da Sani Danja ba yana nufi mun zama makiya ba – Mansurah Isah

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Mansura Isah ta bayyana cewa mutuwar aure tsakaninta da tsohon mijinta Sani Musa Danja hakan baya nuna cewa sun zama abokan gaba.
Mansura Isah ta bayyana haka ga majiyar DCL Hausa ta Daily trust a cikin wata hira da aka yi da ita a karshen mako.
“Ban ga wani abun aibi ba don aurenmu ya mutu.
Sani shi ne uban ‘ya’yana, ga shi dama abokina ne kuma abokin aiki. Don haka, ban fahimci dalilin da yasa mutane ke ta yawan maganganu game da hakan ba. Muna cikin duniyar zamani a yanzu; kasancewar ya sake ni ba ya nufin mu zama makiya” inji Mansura Isah.
Jama’a da dama sun yi mamaki ganin yadda suka fito a cikin wani fim mai suna ‘Fanan’ kasancewar auren su ya mutu a zahiri

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button