Kannywood
Datti Assalafy yayi martani akan sababbin hotunan Maryam Yahaya
Maryam Yahaya bata Karba Shawara - Cewar Datti Assalafy
Advertisment
Shahararren marubucin nan Datti Assalafy yayi magana akan sababbin hotunan Maryam Yahaya bayan samun saukin ta.
Ga abinda yake cewa :-
“Maryam Yahaya an bata shawara ta killace kanta ta dena yada hotunanta a media ta bari sai ta murmure amma taki
Nayi magana da daya daga cikin uwayen dakinta a Masana’antar Hausa film ta tabbatar min da cewa yarinyar bata karban shawara
A cikin wannan yanayi da take ciki abar a tausaya mata ne, Allah kadai ya san wa take son ta burge kuma a media, na san dai ba zata taba burge wadanda suka zalunceta ba domin sun gujeta
Muna bata shawara ta sanya Hijabi idan zata yada hotonta a media, zaifi rufa mata asirin ramar da tayi sakamakon jinyar Typhoid da yake damunta a cewarta
Muna fatan Allah Ya yaye mata.”