LabaraiUncategorized

Karon farko yar jahar kano Shatu Garko sanye da hijab ta lashe sarauniyar kyau

Advertisment
Karon farko yar jahar kano Shatu garbo sanye da hijab ta lashe sarauniyar kyau
Shatu Garko

Wata matashiya ƴar Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya Shatu Garko, ta lashe gasar sarauniyar kyau ta ƙasar karo na 44 da aka kammala a jihar Lagos a ranar Juma’a.

Shatu Garko ce yanzu sarauniyar kyau a Najeriya, bayan da doke yan mata 18 da su ka kai ga zagayen ƙarshe na gasar kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito inda yanzu ta gaji Etsanyi Tukura, daga Jihar Taraba.labarai24 ta ruwaito

Sarauniya Shatu Garko ta bayyana jin daɗinta bisa cikar burinta da kuma samun wannan babbar nasara, ta kuma godewa waɗanda su ka shirya gasar tare kuma da mahaifiyarta bisa goyon baya da karfafa mata gwiwa.
Karon farko yar jahar kano Shatu garbo sanye da hijab ta lashe sarauniyar kyau
“Bani da wani buri da ya wuce ganin na zama sarauniyar kyau ta Najeriya. Ina matukar godiya ga waɗanda su ka shirya wannan gasa, ina godiya ga mahaifiyata bisa goyon baya da kuma karfafa min gwiwa”.
Haka kuma an baiwa Sarauniya Shatu Garko kyautar Naira Miliyan 10 da gida da motar hawa da kuma muƙamin jakadiyar kyau ta Najeriya.Karon farko yar jahar kano Shatu Garko sanye da hijab ta lashe sarauniyar kyau
A ƴan shekarun baya dai jihohin Arewa maso yammacin Najeriya kan ƙauracewa shiga gasar saboda tsaraicin da ake nunawa a bikin na sarauniyar kyau.
Jerin ƴan matan da su ka shiga gasar Sarauniyar Kyau
An soma gasar sarauniyar kyau a Najeriya tun a cikin 1957 da nufin karfafawa mata. Kuma duk shekara ne ake gudanar da gasar tsakanin jihohin kasar nan.

Alkalai ke tantance ƴan takarar daga jihohin ƙasar nan kafin zaben sarauniyar kyau.
Haka kuma duk wadda ta lashe sarauniyar kyau a Najeriya ita ce ke wakiltar kasar a sarauniyar kyau ta duniya.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button