Kannywood: Jaruman da sunka taka leda a shekarar 2021
Lawan Ahmad tsohon jarumine wanda yayi tashe a kannywood sosai kuma ya dade yana fitowa a fina finan hausa ya taso a cikin shekarar 2021 a cikin wani film dinshi mai suna izzar so wanda film din ya daga tauraruwar jarumin sosai, bisa irin fadakarwar da akeyi a cikin film din hakanyasa ake cewa jarumin mai gaskiya kuma dama jarumin yana neman takaraa karamar hukumar bakori
Ummi Rahab itama za a iya cewa tsohuwar jaruma ce wanda ta fito a fina finan kannywood tun tana yarinya karama wanda bayan dawowarta ta fito a cikin film din Farin wata sha kallo daga bisani kuma ta koma fitowa a cikin film mai suna Wuff wanda lilin Baba yake shiryawa, bayan rikicin da sukayi da uban gidanta Adam A Zango wanda har yau basa jituwa a tsakaninsu.
Adam Abdullahi Wato Daddy Hikima sanda ya shigo Kannywood yazo a mai bada kayan da jarumai suke sakawa wanda daga baya saiya fara fitowa a fina finai wanda yake fitowa a bangaren dan daba hakan yasa yayi fice a cikin fina finai irinsu Aduniya, Sanda, Haram Da Farin wata Sha Kallo, sunashi ya zageye kannywood akance mishi Abale Ko Ojo.
Aisha Najamu sabuwar jaruma ce wadda film din daya nunawa duniya wace ita shine Izzar so wanda film din shiyasa ta sami masoya sosai a fadin duniya musamman irin fitowar da takeyi a cikin fim din ta rashin mutunci, jarumar yanzu tana daga cikin kyawawan jaruman kannywood masu tarin masoya wanda itama ta shiga dandalin tiktok yana gabatar da bidiyo kala kala.
Nuhu Abdullahi Shima tsohon jarumi ne wanda ya dade yana fitowa a cikin fina finan hausa amman ya sami Karin daukaka a cikin sabon film maoi dogon zango mai suna LABARINA wanda ya fito a matsayin Mahmud, kuma shine tsohon saurayin Fati Washa wanda yaso ya aureta yayinda ake hira dashi yake cewa zai iya aurenta, amman kuma kawai akaji batun aurenshi da wata.
Nafisa Abdullahi Kamar yadda kowa ya sani Nafisa tsohuwar jaruma ce wadda ta dade sosai a kannywood tayi manya manya fina finai har aka dena yayin jarumar a kannywood sai bayan fitowar shirin LABARINA jarumar ta dawo tashe sosai a kannywood, saide yanzu haka jaruma Nafisa Abdullahi tana kokarin fita daga cikin shirin ko kuma muce tana fice wadda aka samu Fati washa ta maye gurbinta a cikin shirin.
Rabi’u Rikadawa ko kuma muce Baba Dan Audu ya kasance tsohon dan wasan kannywood wanda ya taka rawa sosai a masana’antar kannywood shima ya kara samun daukaka ne a fitowar da yayi a cikin shirin Labarina wanda ya fito a wata fitowa mai burgewa, ya fito a bayan kudi a cikin shirin wanda ake tunanin cewa shi mahaifin Mahmud ne a cikin shirin.