Labarai

Idan Kayan Matan Da Kike Sayarwa Yana Aiki Me Yasa Aurenki Ya Mutu, Attajiri Nwoko Ya Ƙalubalanci Jaruma

Idan Kayan Matan Da Kike Sayarwa Yana Aiki Me Yasa Aurenki Ya Mutu, Attajiri Nwoko Ya Ƙalubalanci JarumaHamshakin ɗan kasuwar nan a Kudu, Ned Nwoko ya fitar da zazzafan martani akan labarin da shahararriyar mai sayar da kayan matan nan Hauwa Sa’idu wato (Jaruma) ta fitar cewar, sakamakon kayan matan da ta bawa amaryarsa ne yasa ya saki uwar-gidansa ƴar ƙasar Marocco Laila Charani.
Sai dai Ned ya mayarwa da Jaruma kakkausan martani, inda ya bayyana cewar, idan har kayan matan da take sayarwa yana tasiri mai yasa ta kasa riƙe mijinta da shi ta bari har aurenta ya mutu.
Muryoyi ta ruwaito Rikici ya kunno kai tsakanin Mista Ned da uwar-gidansa ƴar ƙasar Morocco Laila Charani bayan ya auri jarumar Fina-finai Regina Daniels, har ta kai ga ya saki uwar-gidan tasa.
Faruwar hakan yasa nan da nan Jaruma ta yaɗa cewa haɗin kayan matan da ta bawa Regina ne ya ruɗa shi, kamar yadda majiyar mu ta Muryoyi ta bayyana.
Tun a bara ne dai aka fallasa cewa auren Jaruma da Isabor ya mutu har akayi ta cece-kuce.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA