Addini

Dalilin da yasa nace karta da jin waƙa ba haramun bane – Sheikh Ibrahim khalil

Advertisment

Dalilin da yasa nace karta da jin waƙa ba haramun bane - Sheikh Ibrahim khalilFitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Ibrahim Khalil, ya kare wata fatawa da ya bayar a baya-bayan nan da ke halatta jin waƙa, saɓanin fatawar da malamai da dama takwarorinsa suka sha bayarwa da ke haramta sauraron waƙar.
Sheikh Malam Ibrahim Khalil ya bayyana cewa waƙa ba laifi ba ce a addinin Islama Musulunci, kamar yadda ya shaida wa taron Jami’ar Bayero a Kano na “Ga fili ga mai doki” domin tunawa da fitaccen mawaƙin Hausa Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos wanda Sashen Koyar da Harsunan Najeriya ya saba gabatarwa, a ƙarƙashin jagorancin babban masanin waƙoƙin baka na Hausa a nahiyar Afirka, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.
Malamin, a lokacin da yake jawabinsa na kammala taron da aka gudanar a watan Nuwamba, ya bayyana cewa “kashi 50 cikin 100 na tunanin ɗan Adam, yana cikin waƙa. Don haka duk wanda ya haramtawa kansa waƙa, to ya haramtawa kansa kashi 50 na tunani. Ita waƙa ba laifi ba ce,” in ji shi.
Fatawar malamin ta haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta yaɗa bidiyonsa, wasu na karɓar fatawar, wasu kuwa na ganinta a matsayin wani yunƙuri na shagaltar da jama’a.
Sai dai yayin wata hira da BBC Hausa, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce yana nan a kan bakarsa.
‘Inda za ka san waƙa tsari ne na Allah kuma ɗabi’a ce ta ɗan adam shi ne idan ka ɗauki yaro ɗan shekara ɗaya ko biyu da ka sa masa waƙa za ka ga yana nuna alamar zai yi rawa, yana nuna jin daɗinsa, sannan idan ka dubi duk wani dattijo za ka ga ya haddace wata waƙa ta zamaninsa” inji Malamin.
Ya ƙara da cewa ”Ko da Annabi Muhammad SAW ya saurari waƙoƙii, masu kyau, har ma wata rana ya taɓa cewa wani ya yi masa wakar wane, ya ambaci wanda ba musulmi ba ne ba ma, sai da ya rera masa baiti 100 a waƙar mutumin”
Ya ci gaba da cewa: “baya ga Annabi Muhammad SAW, su ma sahabbai da tabi’ai da yawansu wasu sun yi waƙa, ko kuma sun rera ta, kamar Sayyadina Ali yakan sa a yi waƙa a wajen Majalisa don a samu nishadi, baya ga irinsu Zuhuri da shi ma yakan yi.”
‘Muhimmancin waƙa’
Malamin ya bayyana abubuwan da waƙa ke haifar wa ga rayuwar ɗan Adam.
A cewar malamin ”Nassi da alƙur’ani kamar Suratul Yasin da suratun Shu’ara da suka yi bayani akan waka idan aka duba ƙarshensu za a ga sun tantance tsakanin waƙa mai kyau da kuma mara kyau”
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce hadisan da wasu malamai ke kawowa da zummar haramta jin waƙa hadisai ne da suka yi magana a kan jin wakokin da ba su kamata ba, kamar waɗanda suke yabon caca ko shan giya ko suke suranta mace yadda za a yi sha’awarta, don haka ba wai ana magana ba ne a kan kowacce irin waƙa.
Malamin ya faɗi amfani kusan 10 na waƙa da ya ce bincike ya tabbatar, kamar haka:
Waƙa tana maganin gajiya da samar da kwanciyar hankali da hutu da nishadi da farin ciki
Shekara 2004 bincike ya nuna waka na taimakawa kare gakuwan jiki da kara wa jiki ƙarfi da kare jiki daga abubuwan da ba su dace ba
Wani binciken da aka gudanar a shekarar 2012 ya kara tabbatar da cewa waka da wasan kwaikwayo da rawa cikin jama’a na ƙara wa mutane nishaɗi da kwanciyar hankali, (sai dai ita rawa ba a yarda mata su cakuɗu da maza su yi ba.)..

‘Ni ma ina jin waƙa’
Malamin ya ce shi kansa yana sauraron waƙokin mawaka daban-daban da suka yi shuhura a duniya da zummar nishadantuwa da kuma ɗebewa kansa kewa.
”Duk wata waƙa idan ba ta saɓon Allah ba ce ina son ta, sai dai na fi jin wakoki tsoffin mawakan Hausa, kamar su Narambaɗa, da Salihu Jankiɗi, da Ɗankwairo da Shata, irin su Maidaji Sabon Birni, saboda sun fi hikima, sun fi basira sun kuma fi tunani,” in ji Sheikh Ibrahim Khalil
Malamin ya ƙara da cewa ”Ina sauraron fitattun mawaƙan gambara na ƙasashen duniya irin su James Brows, da Micheal Jackson, da kuma wakoƙin Indiya da sauransu, amma ba na jin waƙokin da ke ɗauke da saƙonnin da basu kamata ba”.
Karta halal ce
Wata fatawa da malamin ya bayar a baya-bayan nan da ta haifar da ce-ce-ku-ce ita ce ta halatta yin Karta, inda a nan ma aka yi ta muhawara, da masu ganin fatawar haka take da wadanda ke ganin akwai kuskure a ciki.
A hirarsa da BBC Hausa, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce ”Karta ba haramun ba ce”
Ya kare matsayarsa cewa inda “karta zama haram shi ne caca, ita ainihin dabara ce ta horar da yaƙi da kuma koyar da mutum yadda zai warware matsala sannan ya jefa abokin gabarsa cikin matsala sannan ya yi nasara a kansa.
”Idan mutum zai yi karta sau daya a shekara ko da matarsa ko da ‘ya’yansa hakan ba laifi ba ne, abun da yake laifi a wajen karta shi ne a yi ca-ca, domin idan ka karanci hotunan da ke jikin karta za ka ga hotunan ne na mayaka da mutanen da suke cikin mulki, sarakuna da waziransu da kwamandojinsu, haka ma lido, da kwado da sauransu”.
Source : Bbchausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button