Labarai
DA ƊUMI-ƊUMI: An samu fashewar bam a gida dubu da filin jirgin sama a Borno
Advertisment
Mazauna rukunin gidaje dubu da ke Maiduguri, Jihar Borno sun tashi da fashewar bam a safiyar yau Asabar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa fashewar bam ɗin ta haifar da tsoro, razani da fargaba ga al’ummar yankin.
Haka kuma jaridar ta ce an harba bam a kan unguwar Gomari Airport, mai tsawon kilomita hudu daga filin jirgin sama da ke birnin Maiduguri.
Daily Trust ta rawaito cewa mazauna unguwannin sun tabbatar da faruwar harin, amma sun ce ba a samu rasa rayuka ba
Jaridar ta kara da cewa wata majiya daga rundunar sojoji ta 33 da ke Njimtelo ta ce dakarun sojoji ne su ka buɗewa ƴan ta’adda wuta da su ka hango su sun shigo gefe-gefen Maiduguri.
Su ma kuma ƴan ta’addan su ka maida martani.