Ashe Kukan Munafuci yakeyi Alƙawalin Petrol ₦65 zuwa ₦340 – Zafaffan sako Sheikh Bello Yabo


Lokaci ya yi da ya kamata ko wanne dan Najeriya ya tanadi bindiga – Sheikh Bello Yabo
Malam Bello Yabo na jihar Sokoto ya yi wani wa’azi mai ratsa jiki wanda mutane da dama su ka dinga cece-kuce akansa.
A wani bidiyo wanda shafin tashar YouTube Al-Annur Media Tv fitaccen Malamin ya bai wa ‘yan Najeriya shawarar mallakar bindiga.
A cewar Malam Bello Yabo, yadda harkar tsaro ta tabarbare a kasar nan, ya kamata ko wanne dan Najeriya ya nemi duk inda ‘yan bindiga su ke zuwa siyo makamai ya siya.
https://youtu.be/OZ0bSqW7AlU
Yaboo
Lokaci ya yi da ya kamata ko wanne dan Najeriya ya tanadi bindiga inji Malam Bello Yabo Sokoto
Kamar yadda yace:
“Mun gano cewa manyan kasar nan ba ta tamu suke yi ba, su na yawo da jami’an tsaro yayin da suke barinmu hakanan.”
Malam Yabo ya ce a gidajen manyan kasar nan akwai masu tsaron lafiyarsu kamar ‘yan sanda da sojoji.
Malamin ya bayyana yadda ya ga motar wani gwamna amma ba na jihar Sokoto ba wanda motoci 5 ne a gabansa yayin da wasu 5 suke bayansa duk don tsaron lafiyarsa saboda rayuwarsa na da muhimmanci.
A cewarsa tunda mu ba mu da masu kula da lafiyarmu, ya kamata mu dage mu nema wa kawunanmu mafita ta hanyar addu’o’i da kuma neman makamai.
Malam Bello Yabo ya kara da cewa matsawar ‘yan bindiga su ka gano kowa a shirye jama’a suke ba za su taba kai hari ba. Hatta sojoji ma kwanton bauna ‘yan bindiga ke yi musu, don sai sun tabbatar su na bacci suke kai musu farmaki.
Ya kara da cewa idan abu ya kai abu, har dazuka za a dinga bin ‘yan bindiga ana kai musu farmaki.
Ya kara da cewa duk wanda ba ya da bindiga ya tanadi gwafarsa wacce zai iya dana wa dan ta’adda a idonsa ya fashe.