Yadda Jaruma Halima Atete Ta taka Rawar Gani A kannywood
Shaharrar jaruma halima yusuf atete wanda tana daga cikin manyan matan masananatar kannywood kuma masu tashe shine munka kawo muku labarin irin yadda ta taka Rawar Gani a masananatar.
Dan jarida kuma ma’aikacin gidan jaridar legit shine yayi kokarin bayyana wannan takaitacen tarin rayuwarta da irin tawa rawar Gani ta tayi a shafinsa na sada zumunta.
“Jarumar Kannywood Halima Yusuf Atete.
An haifi @haleemaatete a ranar 26 ga watan Nuwambar 1988, a garin Maiduguri, jihar Borno.
A shekarar 2012 ta fara fitowa a cikin fina finan Hausa, kuma tayi fina-finai da yawa, amma fim ɗin Ƙona Gari, Asalina da Dakin Amarya su ne suka sa Atete ta shahara.
Ta fi fitowa a matsayin mace mai zafin kishi, marar mutunci ko yar bariki (a cikin fina finai.)
Ta fito a fina finai sama da 160, amma ga wasu kaɗan daga cikin fina finan da Atete ta fito a cikin su:
– Wata Hudu, Yaudarar Zuciya
– Asalina, Kona Gari , Ba’asi
– Dakin Amarya, Matar Jami’a
– Wata Rayuwa, Ashabul Kahfi
– Maidalilin Aure , Mu’amalat
– Soyayya Da Shakuwa , Igiyar Zato
– Alkalin Kauye, Bani Bake
– Kurman Kallo, Uwar Gulma
– Bikin ƴar gata, Alƙalin ƙauye,Labarina.
Tattara bayanai: @sani_ab_hamza“