#Wuff! Ki Agaza Mani Ki Ceto Rayuwata, Ki Tsamoni Daga Kogin Soyayyarki Da Na Fada – Farouq Tukuntawa
Wani matashin saurayi dan kirifto da ke zaune a kano ya aika da sakon Soyayyarsa zuwa ga jarumar wasan kwaikwayo na hausa, Hadiza, inda ya roketa da ta taimaka masa ta ceto rayuwarshi, ta tsamoshi daga kogin soyayyarsa da ya dade da fadawa a ciki.
Jaridar Manuniya ta hango Matashin mai suna Farouq Abdullahi tukuntawa, inda ya aika da sakon soyayyarsa ne a shafin sada zumunta na Facebook inda ya bayyana cewa, ya dade yana so ya bayyana mata irin so da kyaunar da ya ke yi mata ko da kuwa za ta dauki hakan a matsayin shirme.
A zancensa ya ke fadin;”Aminci a gareki. Hajiya Hadiza, hakika na dade ina rokon Allah madaukakin sarki ya nuna min kwatankwacin wannan rana kafin na koma gareshi; Ranar da zan furta maki abun da ya dade a raina ko da kuwa za ki dauki hakan a matsayin shirme, zan yi farin ciki da hakan domin na san na yi wa zuciyata babban gata na fitar mata da ciwon da ta dade ta na dawainiya da ita”.
A sakon nasa, ya kara da cewa;”Hakika sonki ya shiga zuciyata ya ratsa jini da tsokana. Ya yi gunduwa gunduwa da hanjina ya fatattaka koda da tunbina ya ragargaza kayan cikina – ya ratsa hanta, kasusuwa da bargona”.
Daga karshe, matashin ya nemi jarumar da ta agaza masa inda ya ke cewa;” Ki agaza mani ki ceci rayuwata ki tsamoni daga kogin soyayyarki da na fada. Ba na iya cin abinci ba na iya barci ko da na kwanta, hoton kyakkyawar fuskanki ne kawai ya ke mani yawo a idona.
Matashin saurayin, Farouq ya bayyana cewa, rasata daidai ya ke da tarwatsewar dukkanin farin cikinsa tare da cewa, muddin ya sameta, to shi fa ya gama cika burinsa.
Jama’a, wani fata za ku yi wa wannan matashin dan crypto?