Labarai
Wizkid ya lashe kyautar mawaƙa ta Afrika
Advertisment
Mawakin Najeriya mai salon kiɗan Afrobeats ya lashe kyautar mawaƙa ta AFRIMA 2021 a bikin da aka gudanar a ranar Lahadi.
Wizkid ya lashe kyautar mawaƙin shekara, waƙar shekara da kuma waƙar haɗin gwiwa da ta fi shahara kamar yadda bbchausa na ruwaito
Mawaƙin NajeriyaFireboy DML ne ya karɓi kyautar masoya yayin da mawaƙiyar Kenya Nikita Kering ta karɓi kyautar gwarzuwa a salon waƙar RnB.
An gudanar da bikin ne a birnin Lagos, kudancin Najeriya.