Tirkashi: Bidiyon jarumi Sadiq Sani Sadiq yana rawar rashin daraja da wata
Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya shayar da mutane da dama mamaki bayyan bayyanar wani bidiyonsa wanda M13 Novel suka wallafa a tashar su ta YouTube.
https://youtu.be/Vo8PU9Puq30
A bidiyon an ga jarumin sanye da wasu fararen kaya irin na zamani yana kwasar wani rawa na rashin mutunci tare da wata budurwa wacce ta sa itama fararen kaya ta zubo gashin doki har gadon bayanta.
Rawan da suka yi kamar zasu shiga jikin juna shine ya fi tayar wa kowa hankali musamman yadda aka san jarumin da aure da mutuncinsa.
An dauki bidiyon ne kamar a wani gidan wasa don yayin da suke kwasar rawar akwai ihu da jama’a suke yi musu don kara tunzurasu.
Jarumi Sadiq Sani Sadiq fitaccen jarumi ne a Kannywood wanda ya dade kuma mutane da dama suna ganin mutuncinsa, kuma kowa ya san yadda matarsa, Murja Shema wacce kanwa ce ga tsohon gwamnan jihar Katsina bata iya boye soyayyarta a gareshi.
Kwanakin baya aka ga yadda matar tasa ta shirya masa liyafa ta gani da fadi a ranar zagayowar haihuwarsa kuma aka ga yadda ta rungumeshi a bidiyon cike da kauna.