Soyayyar Shan Minti Babban Abun Da Ke Jawo Rashin Zaman Lafiya Da Mutuwar Aure a Ƙasar Hausa
Shin ko me ke jawo hakan? Me yasa samari da ƴan mata ke aikata Soyayyar Shan Minti kamin aure? Waɗanne matsaloli Soyayyar Shan Minti ke haifarwa bayan an yi aure?
Shin ya kamata mace ta saki jiki namiji ya dinga jin daɗi da ita ta fuskar Kissing da Hugging don kar ran shi ya ɓaci a dalilin Soyayyar da ta ke yi masa?
Fitacciyar marubuciyar nan, Fauziyya D. Sulaiman, tare da Malamin Addinin Musuluncin nan da ke Kano Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya, sun yi bayani dalla-dalla game da waɗannan mas’alolin da abun da ke jawo su. A ɓangaren Fauziyya, ta kawo labaran wasu ƴan mata da zawarawa da Soyayyar Shan Minti ta kai su ta baro, a ƙarshe mazan su ka gudu, bayan sun yaudare su, sun samu abun da su ke a wajen su.
Haka nan a ɓangaren Malam Abdallah, shima ya ba da labarin yadda wasu mata da kwaɗayi ya sa su ka faɗa tarkon mazan da su ka yaudare su, wanda a ƙarshe bayan ɗaya saurayin ya sadu da macen har ciki ya shiga, ya tsallake ya gudu tare da canja layin wayan sa.
Domin gani da sauraron cikakken bayanin Malam Abdallah da Fauziyya game da wannan maudu’i na Soyayyar Shan Minti da abun da ya jawowa wasu matan.
Idan akwai wani babban abun da ke tasiri wajen haddasa mutuwar aure, to, Soyayyar Shan Minti (neman juna tsakanin ma’aurata kamin aure) ya na daga ciki. Domin abu ne yanzu da ya zama ruwan dare, yadda mata da maza ke kusantar juna ta fuskar taɓe-taɓe ko ma saduwa kamin aure.
Ga bidiyon nan ku kalla.
https://youtu.be/A1RllTVWOgU