Addini

Shin Ya Hallata Mutum Ya Auri Karuwa? – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin Maɗigo Da Illolinsa A Musulunci - Sheikh Aminu Ibrahim DaurawaIdan mace ta shahara da karuwanci sai kuma daga baya ta tuba shin za a iya auran ta,?
Ko Kuma wani mutum ya shahara da zina shin idan ya tuba za a iya bashi aure?
Akwai wani mutum da suka saba da wata karuwa tun kafin ya musulunta a zamanin jahiliyya, sai bayan musulunci sai suka haɗu da juna sai ta nemi suyi harka sai ya sace mata ya tuba yanzu sakamakon shigar sa musulunci, to sai ta nemi ya aure ta, sai yace sai ya tambayi Manzon Allah saw akan haka, bayan ya tambayi Manzo SAW, sai aya ta sauka tana haka auran karuwa ko mazinaciya da mazinaci duk wanda aka tabbatar cewa mazinaci ne baya halatta aba shi aure, sai ya tuba haka duk wacce aka tabbatar tana zina baya halatta a aure ta sai an tabbatar ta tuba ta gyara halin ta,
Baya halatta mutun ya auri karuwa wacce ta ke tijara da mutuncin ta har sai an sami sharaɗi guda huɗu,
Na ɗaya ya zamanto ta tuba daga karuwancin kuma ta yi nadama,
Na biyu ya zama ta yi istibra’i, don a tabbatar ba ta da ciki ko wani mai kama da haka.
Na uku ayi gwajin lafiya a tabbatar ba ta ɗauke da wani ciwo da ta samu a wajan karuwancin wanda mijin ya na iya ɗauka.
Na huɗu kuma ya zama akwai wata masalaha a cikin yin haka. kuma ba zai zama surutu da ɓatanci ba a gare su musamman a wajan da aka san ta taɓa yin haka. Kuma al’ummar mu idwn mutum ya aikata wani laifi ko ya tuba sai sun ci gaba da aibata shi da wannan laifin.
Allah ya kyauta. Kuma ya shirye mu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA