Maryam Wazeery Lailah Labarina Ta Fadi Wani Sirri Akan Kamfanin Saira Movies
A Lokacin da yake aikewa da Sakon taya murna a wani labarin Mai dauke da bidiyon da Daraktan Fina finan hausa Malam Aminu saira ya wallafa a shafinsa na Instagram a Ranar juma’a Kan auren Jaruma Maryam Wazeery Wacce akafi sani da suna LAILA ta Shirin Labarina Malam Aminu saira Yana Mai cewa A madadina da Kamfanin sairamovies Muna taya “Yar uwa maryam wazeery Murnar Auren da tayi a yau. Allah ya basu zaman Lafiya, Allah kuma ya basu zuriya dayyiba congratulations muna missing din ki LAILA Labarina Inji shi Malam Aminu saira.
dai Jim ka’dan da wannan labari Jarumar tazo Kasan labarin Comment section) na Malam Aminu saira tana Mai Cewa ameen ya hayyu ya qayyum nagode sosai, bazan manta da saira movie ba Inji Jaruma Maryam Wazeery Laila.
Jarumar ‘yar Asalin jihar Gombe an Daura auren ta a Ranar juma’ar data gabata a mahaifarta Dake kaltingo ta jihar Gombe anyi wannan aure ne Babu zato Babu tsammani cikin sirri.
Jaruma Maryam ta samu dauka ne tun Bayan Fara fitowarta a Shirin Labarina na malam Aminu saira.