Kannywood

Kamfanin Spacekraft ya ƙaddamar da manhajar nishaɗantarwa da Hausa ta yanar gizo

Advertisment

Kamfanin Spacekraft Media Limited ya ƙaddamar da manhajar nishaɗantarwa da Hausa ta yanar gizo a yau Juma’a.
A wata sanarwa da Shugabar kamfanin, Maijidda Moddibo ta fitar, an ƙirƙiri kallo.ng ne domin sada masoya nishaɗi, musamman ma masoya fina-finan Hausa da abinda su ke so da ga wayoyinsu na hannu ko na’ura mai ƙwaƙwalwa a gida ko a wajen sana’o’insu.
A cewar shugabar, manhajar Kallo.ng za ta kawowa al’umma daɗaɗan shirye-shirye da sabbin fina-finai, fina-finai masu dogon zango, shirye-shirye na musamman da kuma kaɗe-kaɗe iri daban-daban na Hausa.Kamfanin Spacekraft ya ƙaddamar da manhajar nishaɗantarwa da Hausa ta yanar gizo
Ta yi bayanin cewa masu sha’awar manhajar za su iya shan kallon shirye-shiryenta ta adreshin yanar gizo, ko a sauke manhajar kallo a na’ura mai ƙwaƙwalwa, wayoyin andiroyid ko kuma iOS, wanda zai zo nan ba da daɗewa ba.
“Burin mu shine mu nishaɗantar da ƴan Afrika a cikin nahiyar da kuma waɗan da ke zaune a ƙasashen waje ta hanyar kawo muku kayatattun shirye-shirye domin ci gaban al’adu da mu’amular mu, ta yadda za mu matso da ƴan Afrika kusa da gida ko a ina su ke a faɗin duniya ta amfani da manhajar mu da bata katsewa.Daily Nigerian Hausa  ta tattara bayyanai
Kamfanin Spacekraft ya ƙaddamar da manhajar nishaɗantarwa da Hausa ta yanar gizo
“Tabbas muna sane da irin rawar da fina-finan Hausa ke takawa wajen haɗa kan al’umma ta hanyar sadar da masu kallo daga gurare daban-daban domin ilimantarwa da kuma saka ko kuma kawo canji ga masu kallo da hada kan al’umma domin kawo ci gaban al’adunmu.
“Ko shakka babu Kannywood ita ce uwa-ma-bada-mama a harkar shirya fina-finan Hausa. Da haka ne za mu haɗa hannu dasu domin kawo canji mai kyau ta hanyar haɗin gwiwa da karbar changin da zamani ya kawo,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Wannan ne ya sanya kuna zaune a gidajen ku za mu riƙa kawo muku dina-finai na da waɗan da su ka yi tashe a shekarun da su ka gabata, da kuma na zamani.
“Babu tantama cewa an san hausawa da son nishaɗi, to ga kallo.ng za ta share muku hawayen ku,”
Ta yi ƙarin haske cewa kallo.ng na ƙarƙashin kamfanin Spacekraft, wanda kamfani ne na gida da ya ke mallakar wasu ƴan ƙasa masu ra’ayin ci gaban al’adunsu.
 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button