Labarai
Jami’an Yan sanda sunyi Nasarar Kashe Yellow Magaji (Arushe) Gawurtacen Dan bindiga (hotuna)
Advertisment
A yanzu nan majiyarmu ta samu labarin kashe wani Gawurtacen dan bindiga wanda ake kira da yellow magaji arushe wanda fitaccen jarumi kuma mai bada umurni a masana’antar kannywood Falalu Dorayi ya kawo rahoto ga abinda yake cewa
“Jami’an Yansanda sun yi dirar mikiya Sun harbe YELLOW MAGAJI (ARUSHE)
wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a hanyar Kaduna-Abuja.
A wani hotel da Yan ta’addan ke kwana mai suna SIR JOE GUEST INN, da ke No. 8 titin Sajo, Unguwan Maigero Sabon Tasha, karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.
An samu nasarar kwato makamai daga hannunsu da abin hawa.
Allah ya kara bawa Jami’an tsaronmu nasara. Ya kawo mana karshen masifar.”
Ga hotunan gawar yellow magaji arushe nan.