Addini

GANI YA KORI JI: Sheikh Nuru Khalil Ya Halarci Taron Maulidi Da Yan Dariƙa keyi (bidiyo)

GANI YA KORI JI: Sheikh Nuru Khalil Ya   Halarci Taron Maulidi Da Yan Dariƙa keyi (bidiyo)Babban malamin Izala kuma limamin Masallacin jumma’a dake birnin tarayya Abuja Sheikh Nuru Khalil ya halarci taron Mauludin Manzon Allah SAW a anguwan Hausawa dake Maraba Abuja.
Shehin malamin ya fara da yabo ga Manzon Allah SAW, yayi karatun mai matukar muhimmanci inda ya bayyana soyayyan Manzon Allah SAW a matsayin wajibi ga dukkan Musulmi.
Yayi karantu mu’ujizozin da darajojin Annabi SAW tare da bada kissoshin daban daban a wurin taron Mauludin.
Idan ba’a manta ba a kwanakin baya ne Sheikh Nuru Khalil ya bayyana cewa kada kiyayyan masu taron Mauludin Manzon Allah SAW yasa mutum ya zama makiyan Manzon Allah SAW baka sani ba. Ya kara da cewa shi bai ga abun cece kuce akan bikin murnan Mauludin Manzon Allah SAW tunda masu Mauludin nan suna yi ne don nuna murna da soyayyan Manzon Rahma SAW.
Daga karshe ya kawo hankali al’ummar Musulmai baki daya dasu yi koyi da kyakyawan dabi’u da halaye irin na Annabi Muhammadu SAW a kowanne bangaren na rayuwar su, kuma saka kasar mu Najeriya addu’a akan Allah ya kawo zaman lafiya a ko’ina a kasar mu Najeriya.
Ga bidiyon nan

 Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button