[Bidiyo] Stephanie Jarumar Dadin Kowa Tayi Cikakken Bayyani Kan Wakar Yabon Manzon Allah Da Tayi
Tun bayan bayyanar jarumar a wani bidiyo wanda ta yi shiga irin ta musulmai har da rufe kan ta tana rera wakar yabon Manzon Allah (SAW), mutane da dama suka dinga cece-kuce.
Akwai wadanda su ke ganin kamar ta yi ne don neman suna a wurin mabiyan ta musulmai na shafukan sada zumunta, yayin da wasu kuma su ke ganin ta na da sha’awar musulunci ne.
Sarah Aloysious (Stephanie) ta yi karin bayani a kan wakar Yabon Manzon Allah da ta yi
A wani bidiyo wanda VOA su ka wallafa, jarumar ta bayyana ta na karin bayani dangane da wakar yabon manzon Allah da ta yi.
Kamar yadda jarumar ta ce:
“Kai musulmi ni kirista ce, ban tashi na roki Allah don ya yi ni a kirista ba, hakazalika kai ma musulmi ba ka tashi ka roki Allah ya yi ka a musulmi ba.”
Jarumar ta kara da bayyana cewa, kawai wayar gari kowa ya yi ya gan shi da addinin sa. Ta ce ta na matukar jin takaici idan ta ga musulmi ko kirista ya na zagin wanda su ke da bambancin addini da shi.
Ta kara da cewa kowa na ta ne kuma duk wanda zai so ta ya so ta yadda ta ke.
Ta musanta batun cewa ta yi wakar yanon manzon Allah ne don ta na so ta musulunta, ta ce kawai ta na son kowa ne.
Har ila yau ta musa zargin da ake yi mata na neman jan hankalin jama’a ta hanyar yin wakar. Inda ta ce sam ba haka ba ne.
Ta bayyana cewa ta na son kowa ne ba don addinin sa ba don haka itama ta ke son a so ta a yadda ta ke.
Wannan shine faifan bidiyo da ta bayyana haka.