Bayan aure, Malala Yousafzai ta kammala karatun digiri a jami’ar Oxford (hotuna)
Bayanan da DCL Hausa ta samu na nuni da cewa mai gwagwarmayar neman ƴancin mata Malala Yousafzai ta kammala karatun digirinta na farko a jami’ar Oxford inda ta karanci kimiyyar siyasa da tattalin arziki.
DCL Hausa ta ba da labarin cewa shekaru 9 kenan bayan da jami’an tsaro suka harbi Malala a lokacin da suke zanga-zangar neman a bar ‘ya’ya mata su yi karatun boko a ƙasar Pakistan.
Mai shekaru 24, Malala Yousafzai ta wallafa a shafinta na Instagram cewa ta kammala karatun digirinta inda ta wallafa hotunanta tare da iyalanta, bikin kammala karatun da ya kamata ya gudana a watan Mayun, 2020, amma ya kai har wannan lokacin saboda bullar cutar corona.
Malala dai ta wallafa hotonta da na mahaifinta Ziauddin Yousafzai da mijinta Asser Malik, kammala karatun nata ya zo ne a lokacin da ƴan kungiyar Taliban suka kashe wasu deal bai mata bayan da suka je makarantar boko.