Baba Buhari Kasa A Dawo Mana Da Abba kyari – Datti Assalafy
An jera kwana uku kenan kullun sai masu garkuwa da mutane sun tare matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja sun kashe mutane sannan suyi garkuwa da wasu, bidiyo na gani akan yadda masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka a hanyar, har sojoji guduwa suke, zuwa nan gaba ba wanda ya san mai zai faru kuma, hanyar Kaduna zuwa Abuja ta koma tarkon mutuwa
Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ka sani cewa mutum daya ne cikin jami’an tsaron Nigeria masu garkuwa da mutane suke jin tsoro shine DCP Abba Kyari
Anyi taron dangi an yiwa DCP Abba Kyari mummunan sharri aka dakatar dashi domin a gudanar da bincike, a lokacin da tsaron Nigeria ke matukar bukatarsa, kusan wata biyu da kammala bincike ba’a samu DCP Abba Kyari da laifi ba, sannan an gagara dawo dashi bakin aiki, me hakan yake nufi?
Muna ji muna gani sai anyi yunkurin dawo dashi aiki sai a shashantar da al’amarin, shin ba’a so DCP Abba Kyari ya kalubalanci masu garkuwa da mutane ne ko kuma cin amanar tsaron kasa ake nufi?
Shin da cigaba da dakatar da DCP Abba Kyari da kuma dawo dashi bakin aiki don Allah wanne yafi alheri ga tsaron Nigeria?
Abinda aka yiwa DCP Abba Kyari ya karya lagon duk wani jami’in tsaro a Nigeria da yake da zuciyar jarunta, ba kowani jami’in tsaro bane zai yadda ya sadaukar da lokacinsa da rayuwarsa kamar yadda Abba Kyari yayi saboda ganin irin wulakanci da neman tozarci da aka yiwa Abba Kyarin
Tun da aka dakatar da DCP Abba Kyari matsalar garkuwa da mutane cigaba da karuwa yake, kuma Abba Kyari kadai ya san hanyoyin sirri da yake bi ya karya kashin gadon bayan manyan barayin kasarnan masu garkuwa da mutane, amma saboda makirci aka masa sharri, bincike ya wankeshi daga zargi amma an gagara dawo dashi
Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari kai Allah Ya bawa karfin iko, yau idan kace kar a wuce minti 30 ba’a dawo da DCP Abba Kyari bakin aiki ba an gama
Baba Buhari don Allah Ka sa baki a dawo mana da DCP Abba Kyari, ko hanyar Abuja zuwa Kaduna kadai tana matukar bukatar gudunmawarsa, balle sauran bangarori da ake fama da matsalar garkuwa da mutane
Muna kira ga ‘yan uwa na social media, don Allah mu juya alkalamin rubutun mu wajen tunatar da shugaba Buhari ya sa baki a dawo da DCP Abba Kyari bakin aiki
Muna rokon Allah Ya bawa shugaba Buhari ikon daukar matakin da ya dace