Angelina Jolie Ta kira Kasashen Musulmai Jahilai kan Rashin Na’am da Fim Dinta mai suna ‘Enternal’
Fitacciyar jarumar fina-finan kasar Amurka na Hollywood Angelina Jolie ta caccaki kasashen Musulmi da suka hana haska wani fim na ta da aka fitar a ‘yan kwanakin nan.
Ta kira kasashen Musulmai “Jahilai” saboda sun hana haska fim na ta na kamfanin Marvel, saboda goyon bayan auren jinsi da ake nunawa a cikin fim din.
Fim din wanda ake nuna yadda mutane masu jinsi daya ke sumbatar juna an dakatar da haska shi a kasashen Musulmai da dama da suka hada da kasar Saudiyya, Qatar, Kuwait, Bahrain da kuma Oman.
A kwanakin baya ne dai wata hukumar tace fina-finai ta bukaci kamfanin na Marvel da ya yanke wuraren da ake nuna irin abubuwan da ba su kamata ba a cikin fim din, sai dai kamfanin ya yi kunnen uwar shegu da wannan bukata ta kamfanin.
kamar yadda Labarun hausa da Nbcnews Na ruwaito Angelina Jolie, wacce ta fito a matsayin Thena Abadi a cikin fim din, ta fito ta tofa albarkacin bakin ta kan lamarin. A wata hira da aka yi da ita, ta kira lamarin a matsayin marar dadi, inda ta kuma kira kasashen da suka hana kallon fim din a matsayin “Jahilai”.
A wani bangare kuma, Angelina Jolie ta yabawa kamfanin na Marvels da yaki yadda ya yanke wasu wurare a fim din.
Auren jinsi har yanzu haramun ne a da yawa daga cikin kasashen Musulmai, irin su Saudiyya, Kuwait, Qatar, da sauran su, hukumomin tace fina-finai na kasashen suna bukatar a dinga yanke dukkan wurin dake nuni da auren jinsi a cikin fim kafin su bari a haska shi a kasashen su.
Fim din mai suna “Eternal” shine fim da kamfanin Marvel suka yi na farko dake nuni da auren jinisi, inda ake nuno maza suna sumbatar juna a ciki.
Fim din dai ya samu fitowar manya-manyan jaruman Hollywood, irin su Angelina Jolie, Salma Hayek, Kumai Nanijani, haka shima mawaki Harry Styles ya samu damar fitowa a cikin fim din, inda ya fito a matsayin dan uwan Thanos.
Sai dai kuma wasu majiyoyin sun ruwaito cewa akwai yiwuwar ba wai saboda sumbata da maza ke yi a cikin fim din ne ya sanya aka hana haska fim din a kasashen ba, inda suka ce an hana haska fim dinne saboda kamfanin na Marvel ya saba yin fim dake nuni da cin zarafin Allah da Manzonin sa.