An kashe ƙasurgumin shugaban ƴan ta’addan nan, Dogo Gide
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna, kamar yadda.
Wata majiya ta shaida wa PRnigeria da hausadailytimes cewa an kashe Gide ne a wani rikici da ya kaure tsakanin sa da mataimakinsa, Sani Dan Makama, inda ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi.
Gide da aka kashe ya kasance ɗaya daga cikin ƴan ta’addan da suka addabi jihohin Zamfara, Neja, Kaduna, Katsina da Kebbi, tsawon shekaru.
“Mataimakinsa mai suna Sani Dan Makama ne ya kashe Dogo Gide bayan wata ‘yar karamar rikici da ta barke a dajin Kuyanbana da ya haɗe jihar Zamfara da Birnin Gwari da garin Dogon Dawa,” inji majiyar.