Labarai

An karrama matashi Ali, Musulmin da ya rasa ransa yayin ceton tsohuwa a Amurka

An karrama matashi Ali, Musulmin da ya rasa ransa yayin ceton tsohuwa a Amurka
Wani matashi Ali, musulmi ya rasa ransa yayin kokarin ceto rayuwar wata dattijuwa ya samu jinjina ta musamman.
A ranar Juma’ar da ta gabata, matashi Ali Abucar Ali mai shekaru 20 ya taimaka wa Betty Walsh mai shekaru 82, wacce aka dinga naushi ana datsarta a bakin wani shago da ke kusa da gidanta da ke yammacin London, wurin ya yi kusa da gidan su Ali.
Dama matashi Ali ya na horar da yara kwallon raga ta kungiyarsu ta Chiswick Gators Basketball Club. Lamarin ya auku ne yayin da ana saura sa’o’i kadan Ali ya gama horar da yaran.
An samu fiye da 90,000 Pounds ($120,000) bayan bude wani asusu da aka yi don tuna Ali.
Wani tsohon dan kwallon raga, Michael Kwentoh wanda ya kirkiro Gators Club ya bayyana yadda ya hadu da Ali lokacin shekarunsa 13.
Kamar yadda ya shaida wa Al Jazeera:
“Ali yaro ne mai gaskiya da kula, ban taba haduwa da mutumin kirki irinsa ba.”
“Ban yi mamakin jin labarin matashi Ali ya yi kokarin taimakon tsohuwa ba. Sai dai abinda ya faru da shi bai dace da shi ba, mutum ne mai gaskiya.”
Matashi Ali ya horar da yara masu shekaru tsakanin 6 zuwa 10, kamar yadda Kwenton ya ce. Kuma ya jajirce akan su kwarai.
Yayin da aka bude asusu don tunawa da shi an bayyana wa jama’a cewa an yi rashin dan’uwa mai kirki da hankali.
Wanda ake zargin ya halaka Ali, Norris Henry mai shekaru 37 zai bayyana gaban kotu ranar Litinin akan halaka matashi Ali da ya yi da kuma yunkurin halaka Walsh, kamar yadda Labarun hausa ta ruwaito.
Hakazalika zai bayyana gaban babbar kotun London a ranar Laraba.
Har yanzu Walsh ta na asibiti ana kula da ita bayan an yi mata aiki akan ciwon koda.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button