Abubuwan Sittin 60 Da Suke Kawo Mutuwar Aure – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Wannan yasa shaidan yake kai kawo da zirga zirga da kulle-kulle da kutungyila wajen lalata harkar Aure,
Sabo yasan in Aure ya lalace komai zai iya lalacewa sakamakon lalacewarshi, wannan yasa Malamai da masu bada Tarbiyya da kuma masu lura da al’amuran al-umma suke kara wayarwa da alumma kai, akan sake-saken Aure da kuma hadarinsa sakamakon yakan haifar da rugujewar gida, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tsaro da rashin zaman lafiyar al-umma, don haka mukayi nazari bayan bincike da tattaunawa, da wadanda suka shiga irin wadannan matsaloli, da bibiyar dalilan da suka jawo hakan, musamman lokacin shirin auren Zawarawa da muka gabatar ƙarƙashin gwabnatin jahar Kano
Dan haka muka fitar da Dalilai guda dari (60 ) wadanda muke gani sune ummul aba isin wadannan matsaloli wadanda idan ba a kula da suba za a samu mutuwar aure.
mun kasa wadannan matsaloli zuwa kasha uku (3) :
1. Matsalolin da suke faruwa kafin Aure
2. matsalolin da suke faruwa lokacin Aure
3. matsalolin da suke faruwa bayan Aure
Wadannan matsalolin guda uku a kwai masu zuwa daga ɓangaren mata akwai, akwai masu zuwa daga ɓangaren maza a kwai, akwai masu zuwa daga duka bangarorin guda guda biyu :
Don haka cibiyar mu ta LOVE AND MERCY SCHOOL FOR MARRIAGE COUNSELING
ta ɗauki waɗannan abubuwa ɗaya bayan ɗaya take shirya bitoci akai.
1. Al-Adu
2. Rashin Ilimin Zamantakewar Aure
3. Rashin Zabin Matar Kirki Ta Gari
4. Auren Babu Soyayya Daga Miji Ko Mata
5. Gaggawar Yin Aure Batare Da Mutum Ya Shirya Ba
6. Banbancin Ilimi
7. Rashin Binciken Halin Miji Kafin Aure
8. Rashin Binciken Halin Mata Kafin Aure
9. Matsalar Iyayen Miji
10. Matsalar Iyayen Mata
11. Matsalar Dangin Miji
12. Matsalar Dangin Mace
13. Rashin Tsafta
14. Rashin Iya Kwalliya
15. Rashin Iya Magana
16. Rashin Ciyarwa
17. Rashin Iya Kwanciyar Aure
18. Rashin Adalci
19. Goyon Kaka (Yar Shagwaba)
20. Auren Kisa Wuta
21. Zaman Gidan Haya
22. Ruwan Ido Wajen Neman Aure
23. Auren Bariki
24. Auren Mace Don Kudinta
25. Auren Dole
26. Matsalar Talauci
27. Matsalar Qawaye
28. Zafin Kishi
29. Rashin Haihuwa
30. Rashin Ladabi
31. Rashin Kunya
32. Shaye-Shayen Kayan Maye
33. Qannen Miji
34. Qannen Amarya
35. Abokan Miji
36. Sata
37. Gulma
38. Tsananin Damuwa
39. Rashi Lafiyar Mace Wajen Gamsar Da Miji
40. Rashin Lafiyar Miji Wajen Gamsar Da Matarshi
41. Sharrin Bokaye
42. Rashin Shawara Tsakanin Miji Da Mata
43. Aikin Mace (Ta Zama Yar Kasuwa Ko Ma’aikaciya)
44. Rashin Ilimi Da Samun Wayewa Akan Aure
45. Rashin Daukar Nauyin Iyali Wajen Basu Haqqi
46. Cin Bashi Ayi Aure
47. Yawan Tafiye-Tafiye (Bala Guro)
48. Yawan Zuwa Unguwa
49. Cin Amanar Aure Daga Miji Ko Mata
50. Shigar Da Qawaye Ko Abokai Cikin Harkar Iyali
51. Rashin Kula Da Addini
52. Girman Kan xaya Daga Cikin Ma’aurata
53. Rashin xaukar Aure A Matsayin Ibada
54. Butulci Da Manta Alheri
55. Samun Larura Ko Wani Ciwo Mai Tsanani
56. Yawan Shigar Iyaye Cikin Harkar Aure
57. Al’mubazzaranci
58. Rashin Godiya
60. Mummunan Zato
61. Rashin Nuna Tausayi Da Damuwa Da Juna.
Allah ya daidaita tsakanin ma’aurata. Ya bada zaman lafiyar aure.